Ana zanga-zangar tsige Shugaba Bolsonaro a Brazil
Dubban yan kasar Barzil ne suka gudanar da zanga-zangar neman Shugaban kasar Jair Bolsonaro ya sauka daga madafan ikon kasar saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa a bangaren sayen maganin annobar korona.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar ta Brazil dake fuskantar bincike dangane da tuhumar da ake masa ya yi gum da bakin sa dangane da batun rashawa da ta shafi batun sayo allurar rigakafin cutar korona a ofishin ministan kiwon lafiyar kasar daga wani kamfanin kasar Indiya.
Wannan dai ne karo na uku da jama’a ke fitowa don nuna bacin ran su dangane da batun rashin iya shugabanci daga Bolsonaro.
Akasarin yan kasar na fatar samun sauyi ta fuskar shugabancin Brazil, inda ake hasashen cewar tsohon Shugaban kasar Lula Inacio da Silva kan iya dawowa kan kujerar shugabancin wannan kasa idan an gudanar da sabon zabe.
Masu boren dauke da alluna su na bukatar Shugaban kasar da yayi murabis, yayin da ake ci gaba da samun karuwar mutanen dake mutuwa sanadiyar cutar Covid-19 a kasar ta Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu