Isa ga babban shafi
Brazil-Coronavirus

An ci tarar Bolsonaro na Brazil saboda karya dokar dakile yaduwar Korona

Hukumomin kasar Brazil sun ci tarar shugaban kasa Jair Bolsonaro saboda samun sa da laifin karya dokokin dakile cutar korona da ke ci gaba da yin illa a cikin kasar.

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro.
Shugaban Brazil Jair Bolsonaro. AP - Eraldo Peres
Talla

Gwamnan Jihar Maranhao Flavio Dino ya ce dole shugaban kasar ya biya tarar saboda yadda ya shirya gangamin jama’a ba tare da mutunta dokar da aka kafa a jihar ba.

Dino ya shaida wa jama’ar jiharsa cewar har yanzu dokar hana mutane sama da 100 gangami tana nan, kuma duk wanda ya karya ta zai gamu da fushin hukuma.

Shugaba Bolsonaro na daga cikin wadanda a farko basu yarda da cutar korona ba, har zuwa lokacin da ya kamu da cutar.

Kasar Brazil ce kasa ta biyu da mutane suka fi mutuwa sakamakon kamuwa da cutar, bayan Amurka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.