Isa ga babban shafi
Brazil-Coronavirus

Dubban 'yan Brazil na zanga-zangar neman tsige shugaban kasar

Dubban ‘yan Brazil sun kaddamar da zanga-zangar adawa da gwamnati inda suke neman shugaban kasar Jair Bolsonaro yayi murabus, saboda gazawa wajen dakile yaduwar annobar Korona da ta halaka ‘yan kasar sama da dubu 200.

Masu zanga-zangar adawa da shugaban Brazil Jair Bolsonaro a birnin Sao Paulo.
Masu zanga-zangar adawa da shugaban Brazil Jair Bolsonaro a birnin Sao Paulo. Amanda Perobelli/Reuters
Talla

Zanga-zangar ta Brazil na zuwa a dai dai lokacin da gwamnati ta soma aiwatar da shirin yiwa al’ummar kasar allurar rigakafin cutar ta Korona da kamfanin AstraZeneca ya samar, da ake sa ran kaiwa ga akalla mutane miliyan 2 a zangon farko.

Gwaji ya nuna cewar maganin na AstraZaneca na da tasirin kashi 70.4 wajen dakile cutar Korona.

Alluran rigakafi akalla miliyan 100 Brazil ke fatan samarwa a cikin gida tare da taimakon kamfanin magungunan na AstraZeneca.

Zuwa yanzu akalla mutane miliyan 8 da dubu 700 suka kamu da cutar a Brazil, daga cikinsu kuma sama da dubu 215 sun rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.