Isa ga babban shafi
Duniya

Farin jinin Shugaba Bolsonaro ya zube a idon yan kasar

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro na ci gaba da haduwa da fushin yan kasar, kamar yada wani bincike jin ra’ayin mutan kasar ke dada nuna cewa tagwamashin Shugaban kasar na fuskantar koma baya, sakamakon dake zuwa shekaru biyu bayan hawan sa karagar mulkin wannan kasa ta Brazil.

Jair Bolsonaro tareda rakiyar dan sa  Sanata Flavio Bolsonaro
Jair Bolsonaro tareda rakiyar dan sa Sanata Flavio Bolsonaro Evaristo Sa/AFP
Talla

A dai-dai lokacin da sakamakon ke fitowa kusan kashi 31 cikin dari na al’umar Brazil ke yabawa aikin shugaban kasar mai shekaru 65.

Kusan yan kasar milyan 68 ne yanzu haka ke fama da talauci, wandada kuma cutar Coronavirus ke barrazana a rayuwar su ,kididdiga na nuni cewa kusan mutane 215.000 ne cutar covid - 19 ta kashe tun bayan bulluwarta a kasar ta Brazil.

Rahotanni baya-baya nan na nuni cewa gwamnatin shugaba Jair Bolsonaro ta gaza wajen takaita yaduwar cutar coronavirus a kasar ta Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.