Isa ga babban shafi
Brazil

Coronavirus ba komai bace face 'yar masassara ta mura - Bolsonaro

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro, ya jagoranci gangamin siyasar da dubban magoya bayansa suka halarta a karshen mako.

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro daga tsakiya, yayin gaisawa da dubban magoya bayansa a Brasilia. 24 ga Mayu, 2020
Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro daga tsakiya, yayin gaisawa da dubban magoya bayansa a Brasilia. 24 ga Mayu, 2020 AFP / Evaristo Sa
Talla

Gangamin siyasar na shugaba Bolsonaro ya gudana ne a daidai lokacin da karfin annobar coronavirus ke karuwa a kasar ta Brazil ta fuskokin kisan daruruwan mutanen da take yi a kowace rana, gami da kama wasu dubbai.

Hotunan bidiyon dake yawo a kafafen yada labarai, da sauran kafafen sadarwa na zamani, sun nuna yadda shugaban na Brazil yayi watsi da takunkuminsa na rufe baki da hanci, lokacin da ya bayyana gaban dubban magoya bayansa, wadanda suka yi cincirindo ba tare da kiyaye sharadin tsarin bada tazara ga juna ba, kamar yadda kwararru a fannin lafiya suka bada shawara.

A baya bayan nan dai, shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya sha nanata cewar, annobar coronavirus ba komai bace face ‘yar masassara ta mura, zalika shugaban na cigaba da nuna adawa ga tsarin killace jama’a a gidajensu da sunan dakile yaduwar cutar ta coronavirus, matakin da yace babu abinda zai haifar illa cutar da tattalin arzikin kasa, gami da jefa mutane cikin halin kunci.

Zuwa yanzu, annobar coronavirus ta halaka sama da mutane dubu 22 a Brazil, daga cikin akalla dubu 350 da suka kamu da cutar, abinda ya sanya kasar ta biyu a duniya wajen samun adadin masu dauke da cutar bayan Amurka mai sama da mutane miliyan 1 da dubu 600.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.