Isa ga babban shafi
Brazil

Nahiyar Kudancin Amurka ta zama sabuwar cibiyar annobar coronavirus - WHO

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana nahiyar Kudancin Amurka a matsayin sabuwar cibiyar annobar coronavirus, sakamakon hauhawar adadin wadanda cutar ta kama da kuma mutanen da ta halaka.

Wani hoton da aka dauka daga jirgin sama dake nuna yadda ake haka daruruwan kaburbura domin binne wadanda annobar coronavirus ta halaka a a wajen birnin Sao Paulo dake kasar Brazil.
Wani hoton da aka dauka daga jirgin sama dake nuna yadda ake haka daruruwan kaburbura domin binne wadanda annobar coronavirus ta halaka a a wajen birnin Sao Paulo dake kasar Brazil. AFP / NELSON ALMEIDA
Talla

WHO ta ce yanzu haka annobar ta fi barna a Brazil, inda a ranar Alhamis jumillar adadin mutanen da ta kashe ya kai dubu 20 da 47, kuma ya ninka ne cikin kwanaki 11 kacal, abinda ya sanya kasar zama ta 6 a duniya a tsakanin wadanda cutar tafi kisa a cikinsu.

A bangaren yawan masu dauke da cutar ta coronavirus kuwa, yanzu haka Brazil ce kasa ta 2 a duniya bayan Amurka da Rasha, da adadin mutane sama dubu 310 da suka kamu da cutar.

A dukunle yankin Latin ko Nahiyar Kudancin Amurka da Brazil take, da kuma Caribbean, na da adadin mutane dubu 651 da 198 da suka kamu da coronavirus, daga cikinsu kuma dubu 36 da 7 sun mutu, kuma kasar Brazil kadai ke da kaso 65 zuwa 70 na adadin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.