Isa ga babban shafi
Brazil - Korona

Sanatocin Brazil sun nemi kotu ta dakatar da Bolsonaro daga kafafen sada zumunta

Wani kwamitin Majalisar Dattijan Brazil dake bincike kan matakan da gwamnatin kasar ta dauka wajen yaki da annobar Korona, ya bukaci kotun kolin kasar da babban mai gabatar da kara, da su rufe shafukan shugaba Jair Bolsonaro na kafofin sadarwar zamani, saboda samunsa da laifin yin karya wajen alakanta rigakafin Koronar da kuma kamuwa da cutar Sida.

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro, 07/10/21.
Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro, 07/10/21. REUTERS - UESLEI MARCELINO
Talla

Cikin bukatar da suka mika ‘Yan majalisar Dattijan sun bukaci kotun koli da ta dakatar da shugaba Bolsonaro daga amfani da kafofin sadarwar zamanin da suka hada da YouTube da Twitter da Facebook da kuma Instagram, bayan da bincike ya bankado cewar shugaban na Brazil ya sharara karyar cewa, wani rahoton gwamnatin Birtaniya ya gano cewar mutanen da aka yi wa allurar rigakafin Korona sun fi fuskantar hatsarin kamuwa da cutar Sida wato AIDS.

A cewar ‘yan majalisar na Brazil 11 dake cikin kwamitin binciken da ya shafe watanni shida yana aiki, ba za su iya ci gaba da lamuntar halayyar shugaban kasar nasu ba, dan haka ya zama dole a dauki mataki akansa.

Zalika, ‘yan majalisar sun nemi kotu da ta umurci Bolsonaro da ya yi jawabi ta kafar Talabijin din kasar tare da janye ikirarin karyar da ya yi, in kuma yaki bin umarnin za a rika cin tararsa dala 9,000 ko wace rana har zuwa lokacin da zai bi umurnin.

Kawo yanzu dai kididdiga ta nuna annobar Korona ta halaka fiye da mutane dubu 600 a Brazil, kasa ta biyu da annobar ta fi yi wa ta’adi a duniya bayan Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.