Isa ga babban shafi
Brazil-Coronavirus

Bolsonaro na fuskantar tuhuma kan sakaci a yaki da covid-19

Shugaba Jair Bolsonaro na Brazil na fuskantar tuhume-tuhume 10 da ke da alaka da yadda ya yi sakacin bai wa cutar corona damar yaduwa tare da kisan mutane fiye dubu dari 6 a sassan kasar.

Jair Bolsonaro na Brazil.
Jair Bolsonaro na Brazil. REUTERS - UESLEI MARCELINO
Talla

Bayan shafe tsawon watanni 6 kwamitin da Majalisar dattijan kasar ta kafa yana aikin binciken sakacin yaduwar cutar ta covid-19 da ta yiwa kasar barna fiye da kowacce a yankin na kudancin Amurka, kwamitin ya bukaci hukunta mutane 60.

A tsawon lokaci da kwamitin ya dauka yana bincike tare da sauraron bahasi da kuma ganawa da shaidu kwamitin ya tattara bayanai da ke tabbatar da sakacin Bolsonaro a yaki da cutar ta covid-19.

Acewar kwamitin baya ga Bolsonaro akwai kuma ministoci 5 da suka kunshi masu ci da wadanda suka sauka baya ga ‘ya’yan shugaban 3 dukkaninsu da suka yi karan tsaye ga dokokin yaki da covid-19.

Shugaban kwamitin majalisar dattijan na Brazil da ya jagoranci binciken kan Bolsonaro Sanata Renan Calheiros na jam’iyyar masu tsaka-tsakan ra’ayi ya gabatarwa majalisar kunshin rahoton da suka tattara mai dauke da shafuka dubu 1 da 200.

Sanata Renan Calheiros ya ce dole a tuhuma Bolsonaro da laifukan cin zarafin bil’ada da keta da kuma juya baya ga halin da jama’a ke ciki baya ga sakacin kisan kai bisa sani ko da ya ke tuni Bolsonaro ya yi watsi da rahoton.

Kwamitin y ace al’ummar Brazil na bukatar Bolsonaro ya gurfana don neman yafiyarsu kan laifukan da ya aikata da ya kai ga salwantar daruruwan rayuka.

Tuni dai shugaban y afara gamuwa da kakkausar suka musamman daga kafofin yada labarai na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.