Isa ga babban shafi
Coronavirus

Annobar korona na ci gaba da yaduwa da kisa a duniya

Adadin wadanda annobar korona ta kashe a fadin duniya ya kai miliyan 4,843,739 tun bayan barkewar cutar a China a watan Disambar shekarar 2019, zuwa yammacin Lahadi.

Wani mai dauke da cutar korona a dakin gobe da nisa na wani asabiti a kasar Mauris 7/10/21.
Wani mai dauke da cutar korona a dakin gobe da nisa na wani asabiti a kasar Mauris 7/10/21. Daniel MIHAILESCU AFP
Talla

Alkaluman hukumomin lafiya na cewa Akalla mutane miliyan 237,462,210 suka harbu da cutar coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kiyasin cewa adadin wadanda suka kamu da cutar na iya ninkawa sau biyu zuwa uku fiye da bayanan hukumomin lafiyar kasashe.

A ranar Asabar, an samu sabbin mutuwar mutane 5,425 da sabbin wadanda suka harbu har 351,868 a fadin duniya. Kuma Rasha ke kan gaba da mutuwar mutane 962, sai Brazil mai 404 sai Mexico mai 348.

Amma har yanzu Amurka ita ce ƙasar da cutar ta fi kamari inda mutane 712,974 suka mutu daga cutar cikin mutane 44,317,553.

Brazil ke mataki na biyu inda ta rasa mutane dubu 600,829 cikin 21,567,181, da suka harbu, sai Indiya mai 450,589 cikin 33,953,475, sai Mexico 281,958 sai kuma Rasha mai mutane 216,415 cikin 7,775,365.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.