Isa ga babban shafi
Faransa - Coronavirus

Faransa za ta ninka alluran rigakafin da za ta baiwa kasashe matalauta

Faransa ta ce za ta ninka adadin alluran rigakafin da za ta rabawa kasashe matalauta daga miliyan 60 zuwa miliyan 120.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Shugaba Emmanuel Macron ya yi alkawarin ne a ranar Asabar cikin wani faifan bidiyo birnin a Paris, inda ya ce rashin adalcin da aka yiwa wasu kasashe marasa karfi a bayyane yake, lura da yadda aka bar su a baya wajen yi wa al’ummominsu alluran rigakfin na Korona.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai, Amurka ta ba da sanarwar cewa za ta ninka bayar da tallafin alluran rigakafin cutar Koronar ga kasashe marasa karfi zuwa biliyan 1 da miliyan 100.

Ita ma  kungiyar Tarayyar Turai ta kuduri aniyar rarraba alluran rigakafin cutar har guda miliyan 500 a matsayin tallafi, yayin da shugaba Xi Jinping na China ya lashi takobin samar da rigakafin har guda biliyan 2 nan da karshen shekarar da muke ciki.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wannan cuta ta korana ta lakume rayukan mutane miliyan 4 da dubu 7 da 40 da 525 a sassan duniya tun bayan bullarta a karshen shekarar 2019 a China.

Masana ma na cewa, ainihin adadin mutanen da cutar ta kashe ma ya zarta wanda ake fadi a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.