Adadin mutane da Korona ta kashe a Amurka ya zarta dubu 700
Adadin mutane da annobar korona ta kashe a kasar Amurka ya zarce dubu mutane dunu 700 tun bayan barkewar cutar zuwa ranar Juma'a.
Wallafawa ranar:
Wannan adadi da Jami'ar Johns Hopkins na Amurkan ta fitar shine mafi yawa da aka taba gani a duniya, inda ya yi daidai da yawan jama'ar babban birnin kasar Washington.
Wannan na zuwa ne yayin da adadin wadanda cutar ke kashewa kulla yaumin ke kaiwa sama da dubu 1, a kasar da kashi 55.7 da al’ummarta suka karbi allurar rigakafin cutar.
Korona na ƙara yaɗuwa a Amurka musamman sabon nau’in Delta, inda lamarin ya fi kamari a jihohin kudancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu