Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashe sun ci gaba da matsin lamba ga Isra'ila kan harin Rafah

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da matsa lamba kan Isra'ila ta yi watsi da shirinta na kai farmaki ta kasa a Rafah, inda suka yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta, tare da yin gargadin cewa shirin da ta ke shirin yi zai yi wani mummunan tasiri ga Falasdinawa.

Yankin Rafah na kudancin Zirin Gaza da Isra'ila ta fara kai hare-hare.
Yankin Rafah na kudancin Zirin Gaza da Isra'ila ta fara kai hare-hare. © Ibraheem Abu Mustafa / Reuters
Talla

Ko da a ranar Laraba, Isra’ila ta yi lugudan wuta a kauyukan da ke yankin kudancin Lebanon, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 11 da suka hada da kananan yara 6, ko da yake Isra’ila ta ce mayar da martani ta yi kan harin makamin roka da Hisbullah ta harba mata da ya yi sanadiyyar mutuwar Sojanta guda.

Kungiyar Hisbullah ta Lebanon da Sojojin Isra’ila ya zuwa yanzu sun kwace watanni 4 suna musayar wuta a kan iyakar kasashen biyu.

A Alhamis din nan, Isra'ila ta kaddamar da wani sabon kazamin hari a kudancin Gaza bayan da ta sha alwashin kai wa wani farmaki mai karfi a birnin Rafah mai yawan jama'a duk kuwa da ci gaba da sukar da kasashen duniya suka yi.

Firayin Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce dole ne a ci gaba da shiga Rafah domin samun cikakkiyar nasara.

Netanyahu ya sha alwashin murkushe Hamas a matsayin martani ga harin da kungiyar ta'addanci ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 1 da 160, galibi fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.