Isa ga babban shafi

Isra'Ila ta samu nasarar kubutar da mutane biyu a birnin Rafa dake Gaza

Isra'ila ta sanar da cewa ta ceto wasu mutane biyu da ke hanun Hamas a kudancin birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce kusan Falasdinawa 100 da suka hada da kananan yara aka kashe a wani kazamin harin da aka kai a cikin dare.

ISRAEL-PALESTINIANS/NETANYAHU
ISRAEL-PALESTINIANS/NETANYAHU via REUTERS - POOL
Talla

Isra'ila na shirin kutsawa birnin da ke kan iyaka da Masar ta kasa, inda dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu suka nemi mafaka a sanadin fada da ya barke a arewacin kasar.

Halin da ake ciki na rashin ayyukan jin kai a Rafah ya sanya kungiyoyin agaji da gwamnatocin kasashen waje ciki har da babbar kawar Isra'ila ta Amurka, nuna matukar damuwa kan illar da ka iya haifar da fadada ayyukanta a can.

Da sanyin safiryar yau ne Isra’ila ta sanar da cewa an samu kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a wani samamen da sojojin hadin gwiwa da Shin Bet da kuma 'yan sanda suka kai a Rafah bayan kwashe kusan kwanaki 130 a hannunsu.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana sunayen mutanen biyu Fernando Simon Marman da Louis Har, inda ta ce "Kungiyar ta Hamas ce ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga Oktoba daga Kibbutz Nir Yitzhak". Kuma Dukansu suna cikin kyakkyawan yanayin lafiya, in ji shi.

"Sojoji da na Shin Bet sun dade suna wannan aiki. kuma sun dakata har sai an yi sharuɗɗan aiwatar da shi," in ji kakakin rundunar, Daniel Hagari a wani taron manema labarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.