Isa ga babban shafi

Kungiyoyin kare hakkin dan adam na kokawa game da karuwar zartas da hukuncin kisa a Iran

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun koka game da karuwar mutanen da Iran ke zartaswa da hukuncin kisa saboda laifin zanga-zanga.

Irin yadda iran ke zartas da hukuncin kisa kan wadanda aka kama da laifi
Irin yadda iran ke zartas da hukuncin kisa kan wadanda aka kama da laifi AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta zartaswa da Mohammad Ghobadlou hukuncin kisa da safiyar yau, mutumin da kotu ta dakatar da hukuncin kisan da aka yanke masa da fari saboda cewa an gano yana da tabin hankali.

Matashin mai shekaru 23 na cikin wadanda mahukunta suka kama a 2022 lokacin zanga-zangar adawa da kisan matashiya Mahsa Amini.

An dai kama shi da laifin kisan wani jami’in dan sanda a lokacin zanga-zangar kuma tun a bara kotu ta yanke masa hukuncin kisa, to sai dai bayan da lauyoyin sa suka daukaka kara, kotun gaba ta jingine hukuncin kisa da aka yanke masa, bayan da lauyoyin suka gabatar da shaidun likita dake tabbatar da cewa yana fama da tabin hankali.

Da yake bayani a madadin gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasar Hadi Ghaemi ya ce kisan matashi Muhammad ya sake fito da rashin adalci da gagawar kisan jama’a da mahukuntan kasar ke da shi, yayin da uke burus da umarnin kotuna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.