Isa ga babban shafi

Iran ta fara makoki bayan harin ta'addancin da ya kashe mutane 103 a Kerma

Mahukuntan Iran sun sanar da fara makoki yau Alhamis bayan tagwayen hare-haren bom din da suka kashe mutane 103 jiya Laraba a gab da kabarin Janar Qasem Soleimani wanda Amurka ta yi wa kisan gilla shekaru hudu da suka gabata.

Baya ga mutane 103 da suka mutu akwai kuma daruruwa da suka jikkata.
Baya ga mutane 103 da suka mutu akwai kuma daruruwa da suka jikkata. AFP - -
Talla

Gidan talabijin din Iran ya sanar da fara makokin bayan da Gwamnan lardin na Kerma da ke kudancin Iran Rahman Jalali ya bayyana tashin bama baman biyu da harin ta’addanci.

Harin dai ya faru ne a dai dai lokacin da ake alhinin zagayowar ranar kisan Qasem Soleimani inda mutane suka yi dandazo a gab da qabarinsa kwatsam kuma sai aka samu tashin bom har guda biyu.

Harin ta’addancin da ya kashe mutane 103, ya zo a wani yanayi da ake cike da fargabar tsanantar yaki a gabas ta tsakiya musamman bayan kisan mataimakin jagoran kungiyar Hamas Saleh al-Aruri da Isra’ila ta yi yayin harin da ta kai birnin Beirut na Lebanon a jiya Laraba, babban jami’in da ke matsayin aboki ga Iran.

Kisan na Arouri kari ne kan kisan mayakan Hezbollah har 9 ciki har da Hussein Yazbek da Isra’ilan ta yi duk dai a Larabar, inda jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah ya bayyana cewa mayakansa basa shakkar yaki amma suna kaucewa shelanta shirinsu na kai farmaki, kalaman da ke matsayin karon farko da jagoran ya yi tun bayan kisan Arouri.

Shekara hudu kenan tun bayan da Amurka ta yi wa Qasem Soleimani kisan gilla akan hanyarsa ta dawowa daga Iraqi.

Har zuwa yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin harin na jiya a Iran.    

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.