Isa ga babban shafi

Iran ta aike da jirgin yaki zuwa Tekun Maliya ba tare da bayyana dalili ba

Iran ta aike da katafaren jirgin yakinta na ruwa zuwa tekun Bahar maliya ranar litinin, a dai dai lokacin da takun saka ya tsananta tsakanin ‘yan tawayen Houthi na Yemen da kasashen yammacin Turai, wadanda ke kalubalantar hare-haren da mayakan ke kai wa kan duk wani jirgi da yayi nufin ratsa tekun don isa Isra’ila.

Jirgin yakin kasar Iran na ruwa mai suna  Alborz, wanda ta aike da shi zuwa Tekun Maliya, jim kadan bayan kashe mayakan Houthi 10 da Amurka ta yi.
Jirgin yakin kasar Iran na ruwa mai suna Alborz, wanda ta aike da shi zuwa Tekun Maliya, jim kadan bayan kashe mayakan Houthi 10 da Amurka ta yi. © AP Photo / Fars News Agency, Mahdi Marizad
Talla

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya tabbatar da isar jirgin yakin na Iran tekun Maliya, sai dai kasar ba ta bayyana dalilin girke jirgin ba.

A ranar Lahadin da ta gabata, jiragen yakin Amurka suka nutsar da wasu jiragen ruwan mayakan Houthi tare da kashe 10 daga cikinsu a tekun Maliya, bayan da suka yi yunkurin kama wani jirgin ruwan dakon kaya a nesa da gabar ruwan Yemen.

Tun cikin watan Nuwamban shekarar bara ta 2023, mayakan Houthi ke kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila da kawayenta, farmakin da suka ce ba za su daina kai wa ba, har sai dakarun Isra’ilar sun dakatar da kisan kare dangin da suke yi wa Falasdinawa a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.