Isa ga babban shafi

kwamandojin Iran da Hezbollah na taimaka wa Houthi a hare-haren jiragen ruwa

Wasu majiyoyi a Gabas ta Tsakiya sun ce kwamandojin rundunar juyin juye halin Iran da na Hezbollah suna Yemen, inda suke taimakawa wajen ba wa mayakan ‘yan tawayen Houthi umurni a hare-haren da suke kai wa jiragen ruwa a tekun Maliya.

'Yan tawayen Houthi ssuna kai wa jiragen ruwa hare-hare a tekun Maliya ne don matsa lamba a dakatar da hare-haren Isra'ila a kan Gaza.
'Yan tawayen Houthi ssuna kai wa jiragen ruwa hare-hare a tekun Maliya ne don matsa lamba a dakatar da hare-haren Isra'ila a kan Gaza. AP - Staff Sgt. Donald Holbert
Talla

Iran, wadda ke taimaka wa mayakan Houthi da makamai da kudade ta kara azama wajen samar mata da makamai ne tun bayan da aka fara  yakin Gaza tsakanin Isra’ila da Hamas, kamar yadda majiyoyin suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

 

Kwamandojin na Iran suna taimaka wa mayakan Houthi din ne da bayanan sirri a game da jiragen ruwan da ke tafiya a tekun, musamman wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa Isra’ila.

 

A watan da ya gabata ne Amurka ta yi zargin cewa Iran na da  hannu a hare-haren da ‘yan tawayen Houthi ke kai wa jiragen ruwa a tekun Maliya, kuma bayanan sirrin da ta ke samarwa su na da mahimmanci wajen taimaka wa ‘yan tawaye a hare-haren da suke kai wa jirage.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.