Isa ga babban shafi

Amurka ta ce ta lalata wani makami mai Linzami a yankin mayakan Houthi

Jirgin yakin Amurka ya harbo wani makami mai linzami da mayakan Houthi suka harba daga Yemen,  kan wata cibiyar Amurka da ke aiki a tekun Bahar Maliya, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta sanar. 

Amurka ta ce ta  lalata makamai mai linzami da mayakan Houthi suka harba.
Amurka ta ce ta lalata makamai mai linzami da mayakan Houthi suka harba. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

 

Farmakin dai shi ne na baya-bayan nan da mayakan Houthis ke kai hare-hare kan jiragen ruwan dakon kaya na kasa da kasa da ke ratsa tekun Bahar Maliya, a wani mataki da suka ce goyawa Falasdinawa baya daga kisan gillar da sojojin Isra'ila ke yi a Gaza. 

Hakan dai ya biyo bayan wasu jerin hare-hare ta sama da Amurka da Birtaniyya suka kai kan sansanonin 'yan tawayen Houthi a kasar Yemen, wanda ya janyo barazanar mayar da martani mai zafi daga mayakan da ke samun goyon bayan Iran. 

Da sanyin safiyar jiya Lahadi, mayakan Houthis suka koka da yadda aka ga jiragen Amurka na shawagi kusa da sararin samaniyar Yemen. 

Mai magana da yawun Houthi Mohammed Abdulsalam, ya bayyana shawagin jiragen saman a matsayin keta 'yancin kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.