Isa ga babban shafi

'Yan Yemen sun yi gangamin adawa da hare-haren Amurka da Birtaniya a kasar

A yau juma’a dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birane da dama na kasar Yemen, don nuna bacin rai dangane da hare-haren da jiragen yakin Birtaniya da Amurka suka kai wa cibiyoyin mayakan kungiyar Houthi da ke rike da madafan iko a kasar. 

Masu zanga-zangar nuna goyon baya ga 'yan tawayen Houthi na Yemen a birnin Sanaa.
Masu zanga-zangar nuna goyon baya ga 'yan tawayen Houthi na Yemen a birnin Sanaa. REUTERS - KHALED ABDULLAH
Talla

Masu zanga-zangar wadanda mafi yawansu na dauke da tutar kasar ta Yemen, sun rika rera wake-wake tare da furta kalaman tir ga Amurka da kuma Isra’ila, yayin da daya daga cikin masu zanga-zangar Abdel Azim Ali ke cewa ‘’idan har Amurka da kawayenta za su kaddamar da farmaki a kan mu, to muna cikin shiri’’. 

Majalisar koli da ke jagorantar ayyukan kungiyar ta Houthi mai samun goyon Iran, ta lashi takobin daukar fansa a game da wannan farmaki a kan Amurka da Birtaniya. 

Houthi ta ce daga yanzu ta shelanta yaki a kan muradu da kuma kaddarorin Amurka da Birtaniya, abin da ke nufin cewa dakarun kungiyar za su iya kai musu farmaki a koda yaushe.  

Su dai kasashen biyu sun kaddamar da wannan farmaki a cikin daren jiya ne a matsayin martani dangane da irin hare-haren da mayakan na Houthi ke kai wa jiragen ruwan dakon kaya da ke ratsa tekun Bahar Maliya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.