Isa ga babban shafi

Yemen ta yi alkawarin mayar da martani biyo bayan harin Amurka da Birtaniya

Amurka da Birtaniya za su mori wannan hari da suka kai kasar Yemen," in ji mataimakin ministan harkokin wajen Houthi Hussein al-Izzi a gidan talabijin na Al-Masirah na kasar. Ministan kasar Yemen ya karasa da cewa "kasarmu na fuskantar wani gagarumin hari daga jiragen ruwa na Amurka da Birtaniya,da jiragen sama."

Daya daga cikin jiragen ruwan yakin Amurka a yankin Yemen
Daya daga cikin jiragen ruwan yakin Amurka a yankin Yemen AP - John C. Clark
Talla

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta fitar da wata sanarwa da ta yi cikakken bayani game da harin, ciki har da cewa "an yi taka tsantsan don kaucewa kaiwa fararen hula hari.

Wannan aikin hadin gwuiwa daga Amurka da Birtaniya ya raunata bangaren tsaron kasar Yemen ,ya kuma nuna cewa ikon da 'yan Houthis ke da shi na yin barazana ga sha’anin fatauci da jiragen ruwan masu amfani da wannan hanya za ya fuskanci koma baya.

Yahya Sarre,kakkakin rundunar kasar Yemen
Yahya Sarre,kakkakin rundunar kasar Yemen AFP - MOHAMMED HUWAIS

Rahotanni na bayyana cewa a ranar 11 ga watan Janairu, jirgin sama na Royal Air Force daga Birtaniya tare da goyan bayan dakarun hadin gwiwa sun kai hari kan wasu wurare da bangaren ‘yan tawayen Houthi a kasar Yemen ke amfani da su wajen kai hari a tekun kudancin kasar.

Sojojin kawancen sun gano muhimman na’urori da yan Houthi ke amfani da su  wanda ya keta dokokin kasa da kasa.

Wasu daga cikin hotunan harin Amurka da Birtaniya a Yemen
Wasu daga cikin hotunan harin Amurka da Birtaniya a Yemen AP

Sojojin kawance sun bayyana wani wurin da jirgin su ya kai hari shi ne filin jirgin saman Abbs. Bayanan leken asiri sun nuna an yi amfani da shi wajen harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka a kan Tekun Bahar Maliya.

Amurka da Kasashe kawance sun bayyana kudurinsu na kare hanyoyin teku, wanda kusan kashi 15% na jigilar kayayyaki ke ratsa tekun duniya kuma wanda ke da matukar muhimmanci a bangaren da ya shafi tattalin arzikin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.