Isa ga babban shafi

Amurka da Iran sun yi musayar fursunoni a karkashin jagorancin Qatar

Amurka da Iran sun yi musayar fursunoni biyar-biyar tsakaninsu a yau Litinin, inda Amurkawa biyar da Iraniyawan suka isa kasar Qatar da yammacin nan, bayan fara aikin yarjejeniyar da Qatar din ta jagoranci kullawa tsakanin kasashen biyu.

Amurkawan da Iran ta saki bayan sauka a filin jiragen sama na birnin Doha a kasar Qatar a ranar 18 ga Satumban shekarar 2023.
Amurkawan da Iran ta saki bayan sauka a filin jiragen sama na birnin Doha a kasar Qatar a ranar 18 ga Satumban shekarar 2023. AFP - KARIM JAAFAR
Talla

Amurkawan da Iran ta saki sun hada da Siamak Namazi, da Morad Tahbaz da kuma Emad Shargi, sai kuma wasu biyu da ba a bayyana sunayensu ba, wadanda shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewar nan ba da jimawa ba za a sada su da iyalansu.

Tuni dai itama Amurka ta saki wasu ‘yan Iran biyar da take tsare da su, sai kuma sakarwa kasar kadarorinta na albarkatun mai da a baya ta kwace, wadanda darajarsu ta  kai dala biliyan 6.

Bayanai sun ce biyu daga cikin Iraniyawan biyar da Amurka ta saki ne suka isa Qatar, yayin da ragowar suka zabi ci gaba da zama a Amurkan, ko kuma a wata kasa ta daban a maimakon komawa gida.

Tun a ranar 10 ga watan Agustan da ya gabata, shirin kulla yarjejeniyar musayar fursunonin tsakanin Iran da Amurka ya bayyana, wadda ake sa ran zai sassauta tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, duk da cewar har yanzu suna adawa da juna akan wasu jerin batutuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.