Iran ta ce tana fatan musayar fursunoni da Amurka nan ba da jimawa ba
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce tana fatan tabbatuwar musayar fursunoni da Amurka a Litinin, matsawar ta samu kudaden da suka kai dala biliyan 6, wanda kawar Amurka, Koriya ta Kudu ta rike mata.
Wallafawa ranar:
A karkashin yarjejeniyar, wadda Amurka da Iran suka tabbatar da wanzuwar ta a baya, Iran za ta saki Amurkawa 5 da ke hannunta, kana Amurka ta saki Iraniyawa 5 da ta ke tsare da su.
Kasashen biyu, wadanda ba sa jituwa da juna sun kuma amince da batun sakin kudaden da suka kai dala biliyan 6 mallakin Iran, wanda Koriya ta Kudu ta rike saboda takunkuman Amurka, wanda za tura shi zuwa asusun ajiyar Iran don sayen kayayyakin agaji.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani ya shaida wa wani taron manema labarai a Iran cewa za a yi musayar fursunonin a rana guda, inda za a saki Iraniyawa 5, wadanda Amurka ke tsare daa su.
Kasar Qatar ce ta shirya wannan musayar fursunoni, saboda Iran ba ta da dangantakar diflomasiyya da Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu