Isa ga babban shafi
Iran - Amurka

Ba za mu kyale Iran ta gurgunta tattaunawa kan shirin nukiliyar ta ba - Amurka

Amurka ta yi gargadin cewa ba za ta kyale Iran ta haifar da jan kafa wajen tattaunawar ta da manyan kasashen duniya dangane da makomar shirinta na nukiliya ba, a yayin da kuma a gefe guda take zage damtse wajen gudanar da ayyukanta kan shirin, ta hanyar kara yawan makamashin Uranium da take tacewa.

Hoton Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) dake nuna Shugaban Hukumar Kula da Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya Rafael Grossi da Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, ranar 23 ga Nuwamba, 2021.
Hoton Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) dake nuna Shugaban Hukumar Kula da Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya Rafael Grossi da Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, ranar 23 ga Nuwamba, 2021. - Atomic Energy Organization of Iran/AFP
Talla

Gargadin ya zo ne kwana guda bayan da Amurka ta caccaki Iran, tana mai cewa tattaunawar da take yi da manyan kasashe na tafiyar hawainiya ne saboda da gangan kasar ta Iran ta so hakan.

A ranar Juma’ar da ta gabata aka kammala zagaye na bakwai na tattaunawa kan shirin nukiliyar, bayan kwanaki biyar taron yana gudana a birnin Vienna, kafin ci gaba da tattaunawar a kasar Austria cikin mako mai zuwa.

Cikin watan Yunin da ta gabata ne dai Iran ta dakatar da tattaunawa da manyan kasashe bayan zaben shugaban kasar mai ra'ayin rikau Ebrahim Raisi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.