Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

Iran za ta koma cikin tattaunawar ceto yarjejeniyar Nukiliyarta- Raisi

Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya bude kofar yiwuwar sabunta tattaunawar ceto yarjejejeniyar Nukiliyar da kasar ta kulla tsakaninta da manyan kasashen Duniya duk da cewa sabon shugaban ya gindaya sharudda game da takunkuman Amurka da ke ci gaba da illa ga tattalin arzikin kasar.

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi yayin jawabinsa ga taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi yayin jawabinsa ga taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. HO Iranian Presidency/AFP
Talla

Ebrahim Raisi wanda fitaccen malamin addini ne da ya yi nasarar lashe zaben da ya gabata, ya gaji gwamnatin baya da ke kokarin kyautata alakar kasar da yammacin Duniya, yayin jawabinsa da ke matsayin taron kasa-kasa karon farko da ya halarta ya bukaci Amurka ta cika alkawuran da ta dauka na janye takunkuman karya tattalin arzikin da ke kan Iran kamar yadda ya ke kunshe a yarjejeniyar 2015.

A cewar Raisi Iran a shirye ta ke ta shiga tattaunawa gamsasshiya tsakaninta da kasashen Duniya amma sai idan hakan zai kai ga janye mata ilahirin takunkuman karya tattalin arzikin da ke kanta.

Cikin jawabin na sa wanda ba na kai tsaye ba, ya nanata cewa batun mallakar makaman Nukiliya haramtaccen lamari ne a addinan ce, yana mai cewa basu da wani kudiri na mallakar makamin a yanzu da sunan tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.