Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta ja kunnen masu tunanin kai mata hari

Kasar Iran ta gargadi kasashe da kakkausar Murya a game da yunkurin kai mata hari, kan zargin da ake yi mata na kaiwa wani kamfani mallakin wani dan asalin kasar Isra’ila hari a tekun man.

Shugaban Iran, Ebrahim Raisi.
Shugaban Iran, Ebrahim Raisi. ATTA KENARE AFP/File
Talla

Wannan gargadi na zuwa ne bayan da kasashen Burtaniya da Amurka suka goya wa Isra’ila baya game da zargin da take wa Iran da kai harin, abinda tuni Iran din ta musanta.

A yayin hare-hare da aka kai ta hanyar dasa Bam a cikin wata tanka da kuma zubo wasu bama-baman ta sama mutane da dama sun hallaka, ciki kuwa har da jami’an tsaron Burtaniya.

Tuni dai Fira ministan Burtaniya Boris Johnson ya sha alwashin cewa dole ne Iran ta fuskanci hukuncin laifin da ta aikata, abinda ita kuma Iran din ta sha dammarar cewa a shirye ta ke ta tunkari duk kasar da ta yi yunkurin kai mata harin ramuwar gayya kan  laifin da ba ta aikata ba.

Masu sharhi kan alakar kasashe, dai tuni suka fara bayyana fargabar su a game da wannan al’amari da ka iya kara tsamin dangantaka tsakanin Isra’ila da Iran da dama tuntuni basa ga maciji.

Baya ga kasashen Amurka da Burtaniya ita ma Isra’ila ta sha alwashin rama harin da Iran din ta kai mata ta hanyar da bata zata ba, duk da barazanar da Iran din ta yi na cewa duk kasar da ta yi gigin kai mata hari to kuwa shakka babu zata dandana kudar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.