Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Iran na shirin musayar fursunoni da Amurka

Iran ta ce tana ci gaba da tattaunawa da Amurka kan musayar fursunoni, bayan da  Washington ta tabbatar da cewa, ana kokarin karbo ‘yan kasar da aka tsare a wasu kasashen.

Wani gidam yari a Amurka
Wani gidam yari a Amurka AFP PHOTO / SAUL LOEB / FILES
Talla

Jakadan Amurka a Iran, Robert Malley ya ce shugaba Joe Biden ya kafe game da karbo Amurkawan da ke hannun Iran.

Malley ya tabbatar cewa hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin Amurka na tabbatar da karbo ‘yan kasar da ke tsare a wasu kasashen, yana mai cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da Amurkan ke yi da kasar ta Iran.

Wadannan kalaman na zuwa ne yayin da Iran ta shiga tattaunawa da manyan kasashen duniya a Vienna kan farfado da yarjejeniyar nukiliyarta ta shekarar 2015.

Yarjejeniyar, wacce aka yi game da takaita shirin nukiliyar Iran don sassautawa kasar takunkumi da aka kakaba mata, ta kasance cikin halin mutu kwa-kwai rai kwa-kwai tun lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar a shekarar 2018 inda ya sake sabunta takunkumin a wancan lokacin.

Tun daga lokacin ne kuma  kasar ta Iran ta kara kaimin cafke mutanen da ake zargi da laifin leken asiri.

Kasashen biyu a cikin watan Mayu sun musanta cewa sun kammala yarjejeniyar musayar fursunoni, bayan rahotanni da ke cewa an yi yarjejeniya bayan tattaunawar ta Vienna game da sakin fursunoni hudu daga kowane bangare.

Da aka tambaye shi game da kalaman na Malley, kakakin gwamnatin Iran Ali Rabiei ya tabbatar da tattaunawar kuma ya ce gwamnati na kira da a saki dukkan fursunonin Iran din, ba wai iya wadanda suke tsare a Amurka ba kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.