Girgizar kasa mai karfin maki 5.2 ta afkawa wani yanki na Iran
Girgizar kasa mai karfin maki 5.2 ta afkawa yankin arewa maso gabashin Iran a safiyar yau litinin, ko da ya ke zuwa yanzu babu cikakken bayani kan alkaluman mutanen da suka jikkata ko kuma barnar da girgizar kasar ta yiwa yankin.
Wallafawa ranar:
Mahukuntan Iran sun ce da misalin karfe 8:32 na safiyar yau ne girgizar kasar ta afkawa wani yanki da ke gab da birnin Quchan a lardin Razavi Khorasan wadda ya mamayi wurin da fadinsa ya kai kilomita 6.
A cewar Mahukuntan girgizar kasar ta shafi wani yanki na babban birnin lardin Mashhad da ke gab da iyakar Iran da Turkmenistan, birnin na biyu mafi girma a kasar.
Kungiyar agaji ta Red Cresent ta ce jami’anta na cikin shirin ko ta kwana don tunkarar duk wani kalubale da girgizar kasar ka iya haifarwa a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu