Isa ga babban shafi
Faransa-Iran

Macron ya gana da sabon shugaban Iran kan nukiliya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Iran da ta daina karya yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya.

Tashar nukiliyar Iran
Tashar nukiliyar Iran ATTA KENARE AFP/Archivos
Talla

Macron ya gabatar da  bukatar ce a lokacin da yake zantawa da sabon shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ta wayar tarho.

Da yake bayani, shugaba Macron ya ce, akwai bukatar kasar Iran ta dai-daita sahunta game da yadda take mua’amalantar kasashen duniya kan batun yarjejeniyar nukiliyarta.

Sai dai da yake mayar da martani kan bukatar Macron, Sabon shugaban na Iran ya ce, dole ne duk wata tattaunawar nukiliyar da kasar za ta shiga da koma wacce kasa ce a duniya ta kare muradun Iraniyawa.

Shugaba Raisi ya kara da cewa, kasar da gaske take game da batun samar da tsauraran matakan tsaro a gabar tekun Fasha don kare kanta daga duk wata barazana.

Raisi wanda ya zama cikakken shugaban Iran a makon da ya gabata, ya kuma sha alwashin cewa Iran za ta rika sanya muradunta a gaba a yayin duk wata tattaunawa da za ta yi da kasashen duniya game da makamashin nukiliyarta, kuma ba za ta bari kowacce kasa ta kawo barazana ga hakan ba.

An dai shiga turka-turka kan batun makamashin nukiliyar Iran tun bayan da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi fatali da yarjejeniyar a 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.