Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

Iran na ganawa da kasashen duniya kan nukiliyarta

Shirin nukiliyar Iran ya sake daukar hankali a daidai lokacin da kasar ta shiga  sabuwar tattaunawa da manyan kasashen duniya a yau Litinin a birnin Vienna da zummar farfado da yarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2015.

Iran tare da wasu wakilan kasashen duniya
Iran tare da wasu wakilan kasashen duniya - Iranian Foreign Ministry/AFP
Talla

Gwamnatin Iran ta hakikance cewa, shirinta na nukiliyar ya kunshi zaman lafiya ne zalla, amma masana sun kadu da yadda kasar ke ci gaba da habbaka ayyukanta na nukiliyar.

A karkashin yarjejeniyarsu ta shekarar 2015, Iran da manyan kasashen duniya da suka hada da Birtaniya da Faransa da Jamus da China da Amurka da Rasha sun amince cewa, Tehran ba za ta habbaka sinadarinta na Uranium fiye da kashi 3.67, adadin da ya yi kasa da kashi 90 da aka gindaya kafin fara amfani da makamin nukiliya.

Sai dai tun a cikin watan Mayun shekarar 2019, Iran ta sanar da karya ka’idojin yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen, a matsayin martani ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump wanda ya janye daga yarjejeniyar a 2018 tare da kakaba wa kasar takunkumai.

Wani rahoton baya-bayan nan da Hukumar da ke Sanya Ido kan Makamashin Nukiliya ta Duniya ta fihtar  ya ce, a  yanzu, Iran ta tattara karikitan nukiliya har kilogram dubu 2 da 489.7.

Kazalika Iran din ta fara samar da karafen uranium wanda daya ne daga cikin abubuwan da ake har-hadawa domin kera makaman nukilya kamar yadda Abdrea Stricker, wani masani a wata cibiyar kimiya ta birnin Washington ya fallasa.

A karkashin yarjejeniyar ta 2015, Iran dai ta yi alkwarin cewa, ba za ta samar da irin wannan karfe na uranium ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.