Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

Iran ta gabatar da kudirin farfado da yarjejeniyar nukiliyarta

Iran ta ce ta mika wa kasashen Turai daftarin kudirori guda biyu don kokarin farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015, kamar yadda kasashen Turai da Amurka suka ce lokaci ne mai muhimmanci.

Iran tare da wakilan manyan kasashen duniya a birnin Vienna
Iran tare da wakilan manyan kasashen duniya a birnin Vienna © EU Delegation in Vienna/Handout via REUTERS
Talla

Jagoran masu shiga tsakani Ali Bagheri ya shaida wa gidan talabijin na kasar Iran cewa, shawarwarin sun shafi muhimman batutuwa guda biyu da ke fuskantar yarjejeniyar dage takunkumi da kuma alkawurran da Iran ta dauka na nukiliya.

Wannan na zuwa, kwana uku da fara taron tattaunawa a Vienna, don farfado da yarjejeniyar da aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA), wadda ta bai wa Jamhuriyar Musuluncin damar dage wasu takunkuman da suka kakaba wa tattalin arzikinta.

A ranar Litinin aka koma tattaunawa a Vienna bayan Iran ta dakatar da hakan a watan domin gudanar da zaben shugaban kasa mai ra'ayin rikau Ebrahim Raisi.

Bagheri ya ce yanzu tilas ne daya bangaren ya binciki wadannan takardu sannan ya shirya kansa don yin shawarwari da Iran bisa wadannan bukatu.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce an samu ci gaba a tattaunawar, amma lokaci bai kure wa Iran din ba wajen mutunta jarjejeniyar kera makaman nukiliyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.