Isa ga babban shafi

Iran ta kashe dan kasar mai shaidar zama dan Birtaniya da ta samu da laifin leken asiri

Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan Alireza Akbari dan kasar da ke da shaidar zama dan Birtaniya wanda aka yi yankewa hukuncin kisa a baya-bayan nan bayan samunsa da laifin leken asiri, hukuncin da ya sake janyowa kasar kakkausar suka daga kasashen duniya musamman Birtaniya da sauran takwarorinta kasashen yammacin Turai.

Alireza Akbari, Dan Iran da ke da shaida zama dan Birtaniya da aka zartaswa hukuncin kisa.
Alireza Akbari, Dan Iran da ke da shaida zama dan Birtaniya da aka zartaswa hukuncin kisa. AFP - -
Talla

Yau asabar ne aka rataye Akbari mai shekaru 61, wanda mahukuntan kasar ta Iran suka bayyana shi a matsayin maciyi amanar kasa da ke baiwa Birtaniya bayanan sirri a lamurran da suka shafi tsaron  

Shafin labarai na Mizan ya ruwaito wata sanarwar sashen Shari’ar Iran da ke bayyana matakin na rataye Akbari sai dai ba ta fayyace lokaci ko kuma wajen da hukuncin ya faru ba.

Tun shekaru 2 da suka gabata ne mahukuntan Iran suka kame Akbari wanda ya ke aikin samarwa sashen tsaron Birtaniya bayanan sirri ake kuma biyanshi kudin da ya kai dala miliyan 2.

Tuni dai manyan kasashen duniya ciki har da Birtaniya akan gaba suka caccaki hukuncin na Iran wanda suka bayyana da tsantsar take hakkin dan adam.

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana matukar kaduwa da aiwatar da hukuncin kisan kan Akbari yana mai mika sakon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwansa.

Sunak ya bayyana hukuncin da rashin sanin kima da kuma martabar dan adam yayinda ministan harkokin wajen kasar James Cleverly ya yi gargadin cewa hukuncin na Alireza ba zai tafi a banza ba.

Haka zalika kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta bayyana hukuncin da tsagwaron take hakkin dan adam.

Zartas da hukuncin da Iran ta yi dai na zuwa ne sa’o’i kalilan bayan Amurka ta bi sahun Birtaniya wajen aikewa Tehran gargadi game da shirin aiwatar da kisan kan Alireza Akbari.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.