Isa ga babban shafi

Iran ta sake kashe mutane 2 cikin masu zanga-zangar da ta ke tsare da su

Iran ta sanar da kisan wasu fararen hula 2 da aka samu da laifin kisan jami’an tsaron sa kai yayin zanga-zangar da kasar ke gani kan kisan matashiya Mahsa Amini da ‘yan sandan tabbatar da da’a suka yi a bara.

Masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini.
Masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini. AFP - OZAN KOSE
Talla

Mutanen biyu da sashen shari’ar kasar ya bayyana sunansu da Mohamad Karami da kuma Mohammad Hosseini su ne rukuni na 2 na wadanda Iran ke kashewa tun bayan fara hukunta wadanda aka samu da kisan kai yayin zanga-zangar, lamarin da ya ja hankalin kasashen Duniya.

Ko watan jiya sai da Iran ta kashe wasu mutum biyu da aka samu da makamancin laifin, lamarin da ya janyo mata caccaka daga kasashen Duniya.

A watan Satumba ne aka faro zanga-zangar ta Iran sakamakon mutuwar Matashiya Mahsa Amini da ake zargin ‘yan sandan tabbatar da da’a da aikatawa bayan sun kama ta bisa laifin kin saka hijabi.

Jami’an tsaron Iran na ci gaba da kame ilahirin masu goyon bayan zanga-zangar yayinda suka sha alwashin hukunta su ciki har da wadanda tuni aka yankewa hukuncin daurin rai da rai.

Ko a jiya juma’a sai da mahukuntan na Iran suka kame wani dan jarida da ya yi hira da iyalan wadanda kasar ke tsare da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.