Isa ga babban shafi

Iran ta zartar da hukuncin kisa na farko tun bayan fara zanga-zanga

Iran ta zartar da hukuncin kisa na farko ta hanyar taraya a yau alhamis kan wani matashi mai shekaru 23 Mohsen Shekari, daya daga cikin masu zanga-zangar da ta girgiza gwamnatin kasar tun bayan faro ta watan Satumba, lamarin da ya sanya kashashe da kungiyoyin kare hakkin bil adama yin Allah wadai.

Yankin Mahabad na Iran dake fama da zanga-zanga
Yankin Mahabad na Iran dake fama da zanga-zanga © Réseaux sociaux
Talla

Mohsen Shekari dai an yanke masa hukuncin kisa ne bayan da ya tare hanya da kuma raunata wani jami’in tsaro a farkon zanga-zangar da ta biyo bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini.

Ma’aikatar shari’a ta ce an samu Shekari da laifin yin fada da makami da nufin aikata kisa da ta’addanci da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron a al’umma.

Akwai wasu mutane da dama da suma a yanzu ke fuskantar barazanar hukuncin kisan, bayan da aka yanke musu hukuncin rataya kan zanga-zangar da aka yi a makonnin baya-bayan nan, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil adama suka bayyana.

Shugaban kungiyar kare hakkin bil'adama ta Iran Mahmood Amiry-Moghaddam, ya bukaci manyan kasashen duniya su dauki matakin gaggawa kan lamarin, domin a cewar sa  in ba haka ba, akwai barazanar fuskantar hukuncin kisa ga masu zanga-zangar a kowace rana.

Tuni dai kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus suka yi Allah wadai da wannan hukuncin da aka yankewa Shekari.

Iran na zartar da hukuncin kisa ga mutane duk shekara fiye da kowace kasa a duniya in banda China, inda kungiyar kare hakkin bil adama ta Iran ta ce a bana abin ya yi kamari domin a shekarar nan kadai ta yanke wa sama da mutane dari 5 hukuncin kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.