Isa ga babban shafi

Iran ta yankewa Alireza Akbari hukuncin kisa bisa laifin zagon kasa ga tsaron kasar

Kakakin hukumar shari'ar kasar Iran ya yanke hukunci kisa kan wani mutum da aka samu da laifin yi aikata leken asiri, kamar yadda hukumar shari'a ta sanar a yau Laraba.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Iran
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Iran AFP - ALIREZA MOHAMMADI
Talla

Hukumar ta yankewa Alireza Akbari hukuncin kisa bisa laifin cin hanci da rashawa a doron kasa da kuma zagon kasa ga tsaron kasar saboda yada bayanan sirri suka tabbatar.

Magana ba ta bayar da cikakken bayani kan ranar da aka kama shi da kuma yanke irin ba, wanda kotun koli ta tabbatar da hakan.

A farkon watan Janairu, an zartar da hukuncin kisa ga wasu Iraniyawa hudu bayan da aka same su da da aikata kisa saboda "haɗin kai" da Isra'ila.

Iran ta kan sanar da kama wasu jami'ai da ake zargi da aikata laifukan leken asiri na kasar waje ciki har da Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.