Isa ga babban shafi

Ukraine ta yi watsi da kiran Rasha na tsagaita wuta don masu Kirsimati

Umarnin shugaba Vladimir Putin na tsagaita wuta don bayar da damar gudanar da bikin kirsimati ga mabiya kiristanci masu tsattsauran ra’ayi wato Orthodox ya gaza samun karbu a sassan Ukraine duk da kokarin tilastawar da Rasha ta yi wajen ganin dakarunta basu kaddamar da hare-hare ba, har zuwa safiyar gobe asabar.

Dakarun Sojin Ukraine sun ci gaba da kai mabanbantan hare-hare duk da matakin Sojin Rasha ta karbar umarnin Putin wajen tsagaita wuta.
Dakarun Sojin Ukraine sun ci gaba da kai mabanbantan hare-hare duk da matakin Sojin Rasha ta karbar umarnin Putin wajen tsagaita wuta. AFP - PATRIK STOLLARZ
Talla

Ukraine ta yi zargin cewa matakin Rashan na tsagaita wuta wani salon wayo ne don ta samu damar sake tattara dakarunta don afkawa wasu sass ana kasar.

Tashoshin talabijin na Rasha sun ruwaito cewa dakarun kasar za su ja da baya daga dukkanin yankunan da suke gwabza yaki don gudanar da bikin Kirsimatin har zuwa lokacin da aka kayyade na tsagaita wutar.

Sai dai Ukraine ta yi watsi da matakin Rashan game da tsagaita wuta yayinda ta ce za ta ci gaba da mabanbantan farmaki kan dakarun na Moscow.

A bangare guda shima shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana matakin tsagaita wutar na Putin a wani yunkuri don samun damar lumfasawa daga yakin wanda ya ke ci gaba da samun rashin nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.