Rasha ta tsagaita wuta a Ukraine domin bawa kiristoci damar bikin Kirismeti
Shugaba Vladmir Putin na kasar Rasha ya umarci hukumar tsaron kasar da ta dakatar da hare-haren da take kaddamar wa a Ukraine domin bawa mabiyar darikar Orthodox ta masu tsatssauran ra’ayi damar gudanar da nasu bukukuwan Kirismeti.
Wallafawa ranar:
Matakin na zuwa ne, bayan da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da shugaban addini na kasar Rasha Patriarch Kiril suka yi kira ga gwamnatin Rasha da ta dakatar da hare-haren ta a Ukraine.
Sanarwar da Fadar Kremlin ta fitar, ta ce an umarci sojoji su dakatar da kaddamar da hare-hare har tsawon sa’o’i 26, farawa da misalin karfe 12 na ranar 6 ga watan Janairu.
“Domin bawa mabiyar darikar Orthodoxy da ke da rinjaye a wuraren da muke kai hare-hare, muna kira ga sojojin Ukraine da su tsagaita wuta domin bawa Kiristocin damar zuwa coci a ranar jajiberen Kirismeti da kuma bikin ranar,” in ji sanarwar fadar Kremlin.
Shugaba Erdogan na Turkiya a wata tattanawa ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce gwamnatin Ankara a shirye take ta shiga tsakanin Rasha da Ukraine, domin dawo da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu.
Sanarwar da ofishin Erdogan ya fitar, ta ce Turkiyya ta mika tayin diplomasiyya da ta danganci kawo karshen takaddamar da ake y ikan cibiyar nukiliya ta Zaporizhzhia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu