Isa ga babban shafi

Saudiyya ta sako ‘yan tawayen Houthi sama da 100

Wani jirgin sama dauke da ‘yan tawayen Houthi guda 120 da ake tsare da su a Saudiyya ya tashi a wannan Asabar domin mayar da su gida Yemen a cewar kungiyar bayar da agaji ta ICRC ce ta sanar da haka. 

Tawswirar Saudiyya.
Tawswirar Saudiyya. AFP
Talla

 

Sakin fursunonin yakin da Saudiyya ta yi ya biyo bayan tattaunawar sulhu da aka fara yi domin kawo karshen rikicin Yemen na shekaru takwas da ke gudana a tsakanin Yan tawayen Houthi da Iran ke goya wa baya da gwamnatin kasar da kawancen Saudiyya ke tallafa mata.   

  A karkashin wannan sabon tsarin ta tattauna da aka fito da shi gabanin bukukuwan karamar sallah da za a yi a mako mai zuwa, kimanin fursunonin Houthi 900 ake sa ran hukumomin Saudiyya za su sako domin nuna kokarinsu na samun fahimtar juna. 

Tsohon ministan tsraon Yemen da wani dan uwan shugaban kasra na cikin fursunonin da Saudiyya ta sako a wannan Asabar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.