Isa ga babban shafi

Saudiyya da Yemen sun fara musayar fursunoni

A ranar Juma'ar nan ne, aka fara musayar fursunoni tsakanin Saudiya da ke marawa gwamnatin Yemen baya da mayakan Houthi  masu samun goyon bayan Iran, suka sanar da ajiye makamansu. 

Wakilan kasar Saudiya da na mayakan Houthi yayin taron tattaunawar sulhu a Sanaa babban birnin kasar Yemen, ranar 9 ga Afrilun 2023.
Wakilan kasar Saudiya da na mayakan Houthi yayin taron tattaunawar sulhu a Sanaa babban birnin kasar Yemen, ranar 9 ga Afrilun 2023. © Saba News Agency/Handout via REUTERS
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Larabawa suka fara taro da zummar kawo karshen matakin saniyar waren da suka mayar da Syria tsawon shekaru 12. 

Ministocin da sauran manyan jami’an kasashen Kuwait, Oman, Saudiya, Baharain, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Masar, da Iraqi da kuma Jordan ne suka hallara a birnin Jidda a bisa bukatar Saudiya domin tattaunawa akan janye dakatar da Syria da suka yi daga cikinsu, matakin da suka dauka bayan da gwamnatin Basha Al Assad ta fara amfani da karfi wajen murkushe masu yi  masa bore a shekarar 2011. 

A kasar Yemen kuwa daruruwan fursunonin kazamin yakin da aka shafe shekaru akalla takwas ana gabzawa ne ke shirin sake komawa cikin iyalansu, bayan da a yau Juma’a aka kadddamar da shirin musayar fursunonin tsakanin ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran, da kuma gwamnatin Yemen da Saudiya ke  marawa baya. 

Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta ce tuni jirgin farko dauke da fursunoni 35 ya tashi daga birnin Sanaa da ke karkashin ‘yan tawaye zuwa Aden babban birnin yankin Yemen da ke karkashin ikon gwamnati, yayin da wasu fursunonin 125 suka tashi zuwa yankin ‘yan tawaye don komawa gida. 

Kusan fursunoni 900 ake sa ran yin musayarsu tsakanin bangaren gwamnatin Yemen da ‘yan tawayen na Houthi, nasarar da ta biyo bayan tattaunawar sulhun da ake yi tsakanin bangarorin biyu, wadda kuma kai tsaye ke da nasaba da kokarin gayara alakar da ake yi tsakanin Saudiya da Iran. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.