Isa ga babban shafi
Falasdinawa - Yuhudawa

Amnesty ta zargi Isra'ila da wariya kan Falasdinawa

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta bi sawun sauran kungiyoyi wajen ayyana Isra’ila a matsayin kasa mai nuna wariya, wadda ke yi wa  Falasdinawa kallon kaskanci, matakin da kasar ta Yahudawa ta yi watsi da shi a fusace.

Wani sojan Isra'ila na wulakanta wani karamin yaro Ba-Falasdinu.
Wani sojan Isra'ila na wulakanta wani karamin yaro Ba-Falasdinu. AP - NASSER SHIYOUKHI
Talla

Babbar sakatariyar kungiyar Amnesty, Agnes Callamard ta ce manufofin Isra’ila na nuna wariya, kwace da nuna son kai a dukkanin yankunan da ke karkashin ikonta na nuni da kyamar jinsi irin na Apartheid.

Ana tauyawa Falasdinawa 'yanci

Ta ce ko a ina Falasdinawa suke, walau Gaza, Gabashin Birnin Kudus, da sauran yankunan yamma da kogin Jordan, Israila na mu’ammalantar su ne a matsayin kaskantacciyar al’umma, inda take tauye musu hakokinsu.

Isra'ila ta yi watsi

Ministan harkokin wajen Isra’ila, Yair Lapid ya yi watsi da abin da  ya kira ikirarin Amnesty, yana mai cewa sun yi hannun riga da ainihin abin da ke faruwa, inda ya ce kungiyar ta yi amfani da karaiyayi da kungiyoyin ta’addanci ke yadawa.

A shekarar da ta gabata, kungiyar kare hakkin dan adam ta B’Tselem da ke zaune a isra’ila ta fuskanci caccaka a lokacin da ta bayyana manufofin Isra’ila a matsayin wadanda aka fasalta, kuma suka ginu a kan aiwatar da fifiko ga Yahudawa daga yankin Kogin Urdun zuwa na tekun Mediterranean, kuma sun dace da siffofin wariya ta apartheid.

Tun a shekarar 1967 ne yankunan yamma da Kogin Jordan da Birnin Kudus ke karkashin ikon Israila, inda kimanin Yahudawa dubu dari 7 ke zaune tare da Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.