Human Right Watch ta zargi Facebook da sakonnin cin zarafin jama'a
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch ta zargi Facebook da dandalinsa na Instagram da cire sakonnin cin zarafin Falasdinawa yayin tashin hankali tsakaninsu da Isra'ila a wannan shekara.
Wallafawa ranar:
Zargin ya kara matsin lamba ga katafaren kamfanin sadarwar ta duniya bayan da wani mai fallasa bayanan sirri ya bayyanawa 'yan majalisar dokokin Amurka a ranar Talata cewa akwai bukatar a daidaita tsarin kamfanin.
Falasdinawa sun koka a bainar jama'a game da zargin yin kutse a shafukan sada zumunta a watan Mayu, yayin tashin hankali a birnin Kudus wanda ya rikide zuwa mummunan artabu na soji tsakanin kungiyoyin masu kishin Islama dake harba rokoki daga yankunan Falasdinawa, da Isra'ila wacce ta kaddamar da hare -hare ta sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu