Isra'ila ta sake kama fursunoni Falasdinawa da suka tsere daga gidan yarinta
‘Yan sanda a Isra’ila sun ce sun kama 4 daga cikin fursunoni 6 da suka tsere daga wani gidan yari mai cike da matakan tsaro a farkon wannan mako.
Wallafawa ranar:
Tun bayan tserewar da fursunonin suka yi a ranar Litinin ne rundunar sojin kasar ta baza dakaru a sassan kasar da zummar sake damko su.
Fursunoni 2 da aka sake kamewa a baya bayan nan, wadanda aka same su boye a wata tashar manyan motoci a arewacin Nazareth sun hada da wani fitaccen jagoran ‘yan tsagera.
Zakaria Zubeidi, mai shekaru 45, tsohon jagora ne na mau fafutuka a kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a birnin Jenin, kuma yana cikin wadanda aka sake kamawa bayan sun tsere.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu