Isa ga babban shafi
Iran-Isra'ila

Iran na da hannu a harin jirgin Isra'ila-G7

Ministocin Harkokin Wajen kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya G7, sun ce akwai kwararren hujjoji da ke tabbatar da cewa, Iran na da hannu a harin da aka kai wa jirgin ruwan Isra’ila da ya yi sanadiyyar mutuwar wani sojin Birtaniya da wani dan kasar Romania.

Jirgin da aka kai wa hari
Jirgin da aka kai wa hari AFP - KARIM SAHIB
Talla

Sanarwar da suka fitar bayan kammala taronsu a wannan Juma’a, Ministocin Harkokin Wajen sun ce Iran ta yi amfani da jirgi maras matuki ne don kai wannan hari a ranar 29 ga watan Yulin da ya gabata.

Sanarwar ta ce, wannan hari ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa, kuma ya zama wajibi Iran ta yi wa duniya karin haske dangane da lamarin.

A ranar Larabar da ta gabata, Amurka ta yi zargin cewa Iran ta yi kokarin karkata akalar wannan jirgin ne a daidai lokacin da ya isa gabar ruwan kasar Oman, lamarin da ke neman sake dawo da zaman tankiya tsakanin kasashen yamma da kuma Iran.

Daga watan Fabairun da ya gabata zuwa yanzu, sau da dama Isra’ila da Iran na zargin juna da kai wa jiragen ruwa hare-hare a kan tekun Pasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.