Isa ga babban shafi
Amurka - Afghanistan

Za mu kammala janye sojojinmu daga Afghanistan a karshen Agusta - Biden

Shugaba Joe Biden ya ce dakarun Amurka za su kammala ficewa daga Afhghanista a ranar 31 ga watan Agusta mai zuwa, a daidai lokacin da mayakan Taliban ke ci gaba da kwace muhimman yankunan daga hannun dakarun gwamnati.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. Jim WATSON AFP
Talla

Biden wanda ke gabatar da jawabi da yammacin ranar Alhamis, ya ce har yanzu za a iya dakile yunkurin Taliban na karbe iko da kasar.

Biden ya shaida wa manema labarai cewa bai dauki kungiyar Taliban a bakin komai ba, yana mai bayyana kwarin gwiwa a kan dakarun Afghanistan.

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani.
Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani. AP - Rahmat Gul

A baya bayan nan, shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya ce kasar na fuskantar yanayi mafi tsauri na shiga sabon babin wanzuwarta a daidai lokacin da Amurka da kawayenta ke gaf da janye baki dayan dakarunsu daga kasar, bayan shafe shekaru akalla 20 suna gwabza yaki da mayakan kungiyoyin Al Qaeda da Taliban.

Kalaman shugaba Ashraf Ghani na zuwa ne, a daidai lokacin da kungiyar Taliban ke samun nasarar mamaye karin yankunan kasar cikin sauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.