Isa ga babban shafi
ZANGA-ZANGA

Fusatattun manoma a Faransa sun haddasa cunkoso a birnin Paris

Fusatattun manoma a Faransa, sun dauki hanyar zuwa Paris babban birnin kasar cikin motocinsu, a wata sabuwar zanga-zangar neman karin goyon bayan gwamnati da kuma dokoki masu sauki, yayin da kwana guda ya rage a fara gudanar da babban bikin baje kolin noma a babban birnin kasar.

Manoman Faransa kenan da ke gudanar da zanga-zanga a cikin motocin, gabanin babban bikin baje kolin noma da za a yi ranar 24 ga Fabrairu, 2024.
Manoman Faransa kenan da ke gudanar da zanga-zanga a cikin motocin, gabanin babban bikin baje kolin noma da za a yi ranar 24 ga Fabrairu, 2024. AFP - MIGUEL MEDINA
Talla

Motocin tantan da dama ne suka shiga cikin wata unguwa da ke yammacin birnin Paris dauke da tutoci da ke nuna alamar kungiyar manoman da suka gudanar da zanga-zangar.

Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar sun tsaya a kan wata gada da ke saman kogin Seine, kafin su nufi filin Vauban da ke tsakiyar birnin Paris.

Zanga-zangar ta baya-bayan nan dai ta zo ne makonni uku bayan da manoma suka janye shingayen da suka sanya  a kan tituna a kusa da birnin Paris da sauran wurare a kasar bayan da gwamnati ta ce ta ware sama da Yuro miliyan 400 don magance korafe-korafen su kan karancin kudin shiga da kuma abin da kuma rashin adalci da suka ce suna fuskanta daga kasashen wajen da ke sayen kayayyakinsu.

ayarin motocin sun dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wani dan lokaci a kan babbar hanyar A4, da ke gabashin babban birnin kasar, da kuma wasu manyan titunan Paris da safiyar ranar Juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.