Manoma a Faransa sun yi barazanar kara azama a zanga-zangar da suke yi
Kungiyar manoma mafi girma a kasar Faransa na shirin gudanar da gagarumin zanga-zangar gama gari a cikin makwanni masu zuwa don nuna rashin amincewa da harajin da gwamnatin kasar ta dora a kan man katafilar noma, da kuma yadda ta bari suke shan wahala wajen gogayya da kayayyaki masu araha daga kasashen waje.
Wallafawa ranar:
Kakakin kungiyar ne ya bayyana haka a cikin karshen makon da ya wuce, lamarin da ke fadada zanga-zangar manoma a kudu maso yammacin kasar, wadanda suka datse babbar titi, tare da zuba taki a gine-ginen gwamnati.
Daruruwan manoma da katafilar noma ne ke zanga-zanga a birnin Toulouse dake kudu maso yammacin kasar Faransa, lamarin da ya haddasa cinkoson motoci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu