Isa ga babban shafi

Dubban Faransawa sun yi zanga-zangar adawa da cin zarafin Mata

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Faransa domin kalubalantar matsalar cin zarafin mata, wanda ke zuwa a dai-dai lokacin da aka gudar da bikin ranar ta duniya don yaki da wannan matsala.

Zanga-zangar Mata a Faransa.
Zanga-zangar Mata a Faransa. AFP - BERTRAND GUAY
Talla

Masu zanga-zangar sanye da tufafi ruwan rawaya da ke nuna alamar samar da daidaiton jinsi, sun gudanar da tattaki a birnin Paris da wasu birane na kasar Faransa dauke da allunan da ke da rubutun “ a duk minti 6 ana yi wa mace guda fyade” da ''ku ba ‘ya’yanku mata kariya'' sai kuma wani da ke dauke da rubutun ''a ilmantar da maza''.

A lokacin da daya daga cikin masu zanga-zangar Maelle Lenoir ke ganawa da manema labarai, ta bukaci gwamnati ta ware isassun kudade wajen yaki da matsalar cin zarafin mata da ake samu.

A cewar wasu alkaluma da hukumomin Faransa suka fitar, mata 121 aka kashe a bana kadai saboda wariyar jinsi, idan aka kwatanta da mata 118 da aka kashe a shekarar 2022 da ta gabata.

Toh sai dai a wani bidiyo da shugaba Emmanuel Macron ya fitar, ya ce za su kawo karshen matsalar cin zarafin da mata ke fuskanta, domin a cewar sa ba za su lamunci hakan ba.

A shekarar da ta gabata, 'yan sandan Faransa sun ce sun samu korafe-korafe dubu 244 da dari 300 na rikicin iyalai, mafi yawan wadan da abin ya kuma shafa mata ne, wanda hakan ke nuna yadda aka samu karuwar kashi 15 cikin dari a cikin shekara guda kacal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.