Isa ga babban shafi

Wani mahaifi ya kashe 'yayansa mata guda 3 a Faransa

Duniya – Wani mutum a kasar Faransa ya mika kansa ga jami’an tsaro bayan ya dauki alhakin hallaka ‘yayansa mata guda 3, a wani yanayin da ba’a saba gani ba.

Alamar yaki da cin zarafin mata ta hanyar kisa a Faransa
Alamar yaki da cin zarafin mata ta hanyar kisa a Faransa AP - Kamil Zihnioglu
Talla

‘Yan sanda da masu gabatar da kara sun ce mutumin mai shekaru 41 ya yi tataki zuwa ofishin jami’an tsaron ne dake garin Dieppe inda ya shaida masu cewar shi ya kashe ‘yayan nasa mata guda 3.

Masu gabatar da kara da kuma ‘yan sanda sun ce sun samu gawarwakin ‘yayan nasa guda 3 a gidansa dake garin Alfortville a kudu maso gabashin birnin Paris.

Mai gabatar da kara a Paris ya tabbatar da kisan yaran wadanda aka bayana cewar ‘yan shekaru 4 da 10 da kuma 11 ne.

‘Yan sandan sun ce biyu daga cikinsu an daba musu wuka ne wajen hallaka su, yayin da aka lullube gawarsu, sai kuma ta 3 da aka kashe ta a kan kujera.

Majiyar ‘yan sanda tace an taba samun mutumin da laifin tashin hankali a tsakaninsa da iyalinsa a shekarar 2021, abinda ya sa alkali ya bashi umurnin kiyayewa, amma kuma daga bisani aka janye umarnin.

Mai gabatar da kara yace yanzu haka ‘yan sanda na tsare da mutumin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.