Isa ga babban shafi

'Yan Majalisar Faransa sun jagoranci zanga-zangar adawa da kyamar Yahudawa

Fiye da mutane 100,000 ne suka fito a wannan Lahadin da  don gudanar da zanga-zangar adawa da kyamar Yahudawa a birnin Paris, bayan shafe kwanaki ana tafka muhawara tsakanin 'yan kasar da jam’iyyun siyasa kan wanda ya kamata ya shiga tattakin, sakamakon karuwar kyamar Yahudawa a fadin Faransa.

Masu zanga-zangar adawa da kyamar Yahudawa a Paris na kasar Faranasa-12/11/23
Masu zanga-zangar adawa da kyamar Yahudawa a Paris na kasar Faranasa-12/11/23 © CLAUDIA GRECO / REUTERS
Talla

 

Hukumomin sun ce kimanin mutane dubu 105 suka amsa kirar da kakakin majalisar dokokin kasar Yaël Braun-Pivet da takwaransa na dattijai Gérard Larcher, suka yi na fitowa  zanga-zangar adawa da karuwar kyamar Yahudawa a Faransa.

Ministan harkokin cikin gidan Faransa Gérald Darmanin ya ce, fiye da 'yan sanda da jandarmomi 3,000 ne aka girke a babban birnin kasar don tabbatar da tsaro a gagarumin tattakin".

Emmanuel Macron

Shugaban Faransa Emmunel Macron, tun a ranar Asabar ya sanar da cewa ba zai bi sahun masu zanga-zangar ba, amma zai yi hakan ne kawai cikin zuciyarsa ba tare da wani tattaki ba.

Le Pen

Sai dai jagorar masu tsattsauran ra'ayi Marine Le Pen ta bi sahun masu zanga-zangar kamar yadda ta sanar da tun farko, wanda ya haifar da cece-kuce daga jam'iyyun siyasa a daidai lokacin da matsalar kyamar Yahudawa ke neman zama ruwan dare a sassan Faransa.

Goyon bayan Falasdiwa

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da wasu mazauna kasar suka gudanar da zanga-zangar goyan bayan Falasdiwa da kuma adawa hare-haren da ake kai musu a yankin Gaza.

Masu zanga-zangar adawa da hare-haren Isra'ila kan Gaza. 11/11/23
Masu zanga-zangar adawa da hare-haren Isra'ila kan Gaza. 11/11/23 © CLAUDIA GRECO / REUTERS

Yanzu haka ana zaman dar-dar a birnin Paris mai dimbin al'ummar Yahudawa da musulmi, tun bayan harin da kungiyar Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka shafe tsawon wata guda Isra’ila na kai hare-hare a zirin Gaza.

Alkaluma sun nuna cewa an samu kymar Yahuda a Faransa sau 2,250 tun bayan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.