Isa ga babban shafi

Faransawa sun sake fita zanga-zangar adawa da muzgunawar 'yan sanda

Dubun dubatar masu fafutukar yaki da nuna wariya da kuma cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa jama’a ne suka gudanar da wani gangami yau Asabar a Faransa don kalubalantar yadda matsalar ke ci gaba da ta’azzara.

Wasu masu zanga-zanga a birnin Paris na Faransa.
Wasu masu zanga-zanga a birnin Paris na Faransa. AP - Michel Euler
Talla

Masu gangamin dai sun kunshi kungiyoyin masu yaki da nuna wariya, da masu adawa da cin zarafin ‘yan sanda sai kuma masu fafutukar kare hakkin bakin haure kana iyalai da ‘yan uwan wadanda suka gamu da matsalar cin zarafin ‘yan sandan na Faransa baya ga masu yaki da matsalar rashin gidaje da kuma matsalar tattalin arziki.

An dai gudanar da zanga-zangar ne karkashin tsauraran matakan tsaro saboda kaucewa fuskantar tashin hankali makamancin wanda ya biyo bayan kisan matashi Nahel Merzouk mai shekaru 17 da ‘yan sandan na Faransa suka yi a watan Yunin da ya gabata.

Tun bayan mika takardun neman umarnin gudanar da mabanbantan gangamin har guda 100 a sassan Faransa ne, ministan cikin gida Gerald Darmanin ya yi umarnin jibge wadatattun jami’an tsaro a dukkanin yankunan da gangamin zai gudana.

Wasu alkaluma na nuna cewa an jibge 'yan sandan da yawansu ya haura dubu 30 a sassan Faransa, don dakile duk wata barazanar tsaro da ka iya faruwa a lokacin gangamin.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da yadda masu zanga-zangar suka gudanar da gangamin a fusace amma babu rahoton jikkata ko aragama tsakaninsu da jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.