Masu zanga-zanga sun kona gidan wani magajin gari a Paris
A Lahadi, Fira minister Faransa, Élisabeth Borne ta yi tir da harin da masu zaga-zanga suka kai gidan wani magajin gari na wani birni a kewaye birnin Paris, inda har suka banka wa gidan wuta, harin da ta bayyana a matsayin abin takaici.
Wallafawa ranar:
Borne ta yi kira da a hukunta wadanda suka aikata wannan aika aika a gidan magajin garin L’Hay-Les Roses, Vincent Jeanburn.
Jeanburn ya ce mai dakinsa da ‘yayansa biyu, masu shekaru 7 da 5 sun samu rauni a yayin da suke tserewa daga wannan farmaki da masu zanga zanga suka kai musu.
Da take ziyarar birnin na L’Haÿ-les-Roses a ranar Lahadi, Fira ministar ta ce ba zai yiwu a kyale wadanda suka aikata wannan mummunan aiki ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu